<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Na Ji Kiranka, Ya Mai Cetona LW179</title>
<lyrics>[V1]
 1) Na ji kiranka, ya Mai Cetona,
 Na ji zancen ƙaunarka,
 Da gafararka daga zunubi
 Da ka yi dominmu duk.

[V2]
 KORUS
 I, zan bi ka, ya Mai Cetona,
 Zan dai kama hanyarka,
 Yau na zo wurinka domin gafara,
 Sai ka ji roƙona yau.

[V3]
 2) Na gaji da bin hanyoyin Shaiɗan
 Na gaji da bautarsa,
 Ba ya kyauta wa masu binsa fa,
 Mutuwa ce ladansa.
 Korus

[V4]
 3) Ina neman murna da kwanciyar rai,
 Ina neman gafara,
 Ban same su ba cikin duniya
 Sai a wurinka kaɗai.
 Korus

[V5]
 4) Duk wahalar duniya da zafinta
 Wanda Masu Bi ke ji,
 Ba ya kai ga bege na daraja
 Wanda ya ke cikinka.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>179</hymn_number>
</song>